Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta sakin sama da tan dubu 102 na nau’in hatsi iri-iri daga asusun ajiyar abinci na kasa da kuma kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya.
An ce umarnin wani martani ne na wucin gadi da gwamnatin ta yi kan matsalar karancin abinci da ake fama da shi a kasar da kuma tsadar kayayyaki.
Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da tambayoyi daga manema labarai na fadar shugaban kasa, jim kadan bayan kammala taron kwamitin shugaban kasa kan agajin abinci da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja ranar Alhamis.
Ya ce Shugaban kasa ya ba da umarnin a samar da abinci, duk abin da za a dauka.
Matakin dai ya biyo bayan zaman tattaunawa da kwamitin ya yi, dangane da zanga-zangar da ‘yan Najeriya suka yi kan tsadar abinci da sauran kalubalen tattalin arziki.
Idris ya ce, “Na farko shi ne an umurci ma’aikatar noma da samar da abinci da ta saki kimanin Tan 42,000 na masara, gero, garri, da sauran kayayyakin masarufi a cikin dabarun da suka tanada domin samar da wadannan kayayyaki ga ‘yan Najeriya; Tan 42,000 nan take.
Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye
https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx
Torawa Yan'uwa Da Abokai