Photo credits: kwankwasiya Facebook page
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, ya ce gwamnatin Abba Yusuf za ta sake duba dokar kafa masarautun Kano.
Labaran Gari ya waye ya ruwaito cewa bayan nasarar Yusuf a Kotun Koli, an yi ta yada jita-jitar cewa zai iya sauya dokar da ta kafa masarautun biyar.
Kuma da yake magana a wata hira da ya yi da gidajen rediyo a Kano ranar Juma’a, tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP ya ce tabbas za a sake duba dokar.
“A gaskiya, yana daya daga cikin abubuwan da babu wanda ya sanar da ni har yanzu. Amma na tabbata gwamnati za ta sake duba lamarin gaba daya ta kuma yi abin da ake bukata.
“Gwamnatin da ke yanzu za ta ga yuwuwar ko akasin haka ta ba da damar masarautun biyar, ban sani ba. Abin da na sani shi ne, ko shakka babu gwamnati za ta sake duba lamarin,” in ji Sanatan.
Kwankwaso ya bayyana cewa, tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, ya mayar da masarautun ne domin manufarsa ta siyasa.
Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye
https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx
Torawa Yan'uwa Da Abokai