KanunLabarai

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Garkame Kantin Sahad Store

Gari ya waye ta ruwaito cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne Hukumar Kare hakkin masu sayen kaya ta Tarayya, ta rufe Sahad Store, wani shahararren kantin sayar da kayayyaki da ke unguwar Garki a Abuja.

Hukumar ta FCCPC ta ce an rufe shagon ne saboda rashin nuna gaskiya kan yadda yake kayyade farashin kayayyakin.

Wannan dai na zuwa ne sa’o’i ashirin da hudu bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana shirye-shiryen magance matsalolin da ke haddasa matsalar karancin abinci a fadin kasar nan.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnonin jihohi suka amince da kafa wani kwamiti da zai magance matsalar tabarbarewar kayayyaki a kasar.

Domin samun labarai da dumi-dumin su. Latsa wannan link.👇🏻👇🏻👇🏻

https://t.me/labarangariyawaye

Facebook page:

https://www.facebook.com/profile.php?id=61555682938654&mibextid=9R9pXO

X page:

https://x.com/gariyawaye01?t=iPkME2Ddq50H0i5Qf20phw&s=09

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *