KanunLabarai

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya .ta mayar da hedikwatar hukumar filayen jiragen sama na Najeriya zuwa Legas

Gariyawaye ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya zuwa Legas.

 Hakan ya fito ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Manajan Daraktar FAAN, Mrs Olubunmi Kuku.

 Takardar nacewa:

 “Mai girma ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya ya bayar da umarnin mayar da hedikwatar hukumar kula da filayen jiragen sama ta kasa (FAAN) daga Abuja zuwa Legas.

Duba da abin da a rubuta a sama, ana buƙatar ku bayar da tasirin da wannan ƙaura ga hukumar gudanarwa”

 Bayanin ya kasance ranar 15 ga Janairu, 2024.

Torawa Yan'uwa Da Abokai

One thought on “DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Tarayya .ta mayar da hedikwatar hukumar filayen jiragen sama na Najeriya zuwa Legas

  1. Gaskiya bama goyon Baya Amastsayina Na Dan Arewa Anaso Akashe Arewa kenan yakamata Senate da kuda Yan majalisa kuyi magana Akan wannan lamari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *