KanunLabarai

Da Dumi-Dumi: Zanga-zanga ta barke a Nasarawa kan hukuncin Kotun Koli

Gariyawaye ta rawaito cewa zanga-zanga ta barke a garin Lafia babban birnin jihar Nasarawa biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke na tabbatar da zaben gwamna Abdullahi Sule.

Hanyar Lafia zuwa Jos gaba daya ta rufe yayin da magoya bayan jam’iyyar PDP suka kona tayoyi a gaban sakatariyar jam’iyyar ta jihar, inda suka tare hanyar.

 Zanga-zangar ta tilasta wa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyi a cikin Lafia, babban birnin jihar.

 Akwai jami’an tsaro da ke dawo da kwanciyar hankali tare da tabbatar da babu wani tashin hankali.

Shaguna da wuraren kasuwanci da suka hada da makarantu a cikin birnin Lafia sun rufe ba zato ba tsammani.

 

Fasara daga Gistmate.com

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *