KanunLabarai

Dan Kasar China yana rokon Adalci da Tausayawa a Hukuncin da za’a yanke masa akan Kisan Budurwarsa da yayi a Kano

Dan kasar China, Frank Geng Quangrong da ake zargi da laifin kisan budurwar sa, Ummulkhulsum Sani Buhari, ya musanta cewa ya kashe ta ne da gangan, ya kuma roki mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji na babbar kotun jihar Kano da ya tausaya wa shari’a.

A cikin shaidar da ya bayar a ranar Talata, Quangrong ya yi ikirarin cewa ya daba wa budurwar sa wuka ne domin kariyar kai bayan da ya yi zargin ta damke masa ya’yan maraina a watan Satumban 2022.

“Ban kashe Ummulkhulsum da gangan ba amma na daba mata wuka don kare kaina,bayan ta damke min ya’yan maraina” in ji Ouangrong.

Ya roki kotun da ta yi adalci da jin kai a hukuncin da zata yanke.

Ya kara da cewa “Ina son wannan kotu mai daraja ta yi wa shari’a adalci tare da jin kai a cikin hukuncin saboda gaskiyar da na fada a baya.”

Jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa Quangrong ya kashe tsohuwar budurwar sa, Ummulkhulsum, biyo bayan wata rashin fahimta da aka samu a Kano.

Lokacin da aka saurari karar a gaban kotu a ranar Talata, Mai shari’a Ado Ma’aji ya sanya ranar 29 ga Maris, 2024 a matsayin ranar yanke hukunci kan tuhumar da ake yi masa na kisan kai.

Kotun ta tsayar da ranar yanke hukuncin ne bayan da masu gabatar da kara da kuma lauyoyin masu kara suka gabatar da shaidun su na karshe a rubuce.

Lauyan mai gabatar da kara ya kira shaidu shida da za su goyi bayan zargin kisan gilla, kamar yadda sashe na 221 (b) na kundin laifuffuka, kan Quangrong.

Shaidu masu gabatar da kara, wadanda suka hada da mahaifiyar marigayin da ‘yar uwar marigayin, makwabcinsa, likita, da Jami’an ‘yan sanda masu bincike, sun ba da shaida kan abubuwan da suka faru tsakanin Quangrong da Ummulkhulsum, musamman a ranar 16 ga Satumba, 2022.

A lokacin shaidarsa, Quangrong ya musanta kashe Ummulkhulsum da gangan.

Shi ma wani mai ba da shawara kan aikin yoyon fitsari, Dokta Abubakar Abdullahi, shi ma ya shaida a matsayin wanda aka akewa da sammaci.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Facebook page

https://www.facebook.com/profile.php?id=61555682938654&mibextid=9R9pXO

X Page

https://x.com/gariyawaye01?t=iPkME2Ddq50H0i5Qf20phw&s=09

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *