KanunLabarai

DUMI-DUMI: Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya Gayyaci Tsohon Gwamna Ganduje, Shekarau da Kwankwaso domin kafa sabuwar majalisar Dattawan kano

Sanarwar wadda mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi, ta zo ne a daidai lokacin da kotun koli ta tabbatar da Yusuff a matsayin zaben gwamnan Kano a ranar jumaa data gabata.

 Majalisar za ta ƙunshi kwararru, wadanda suka hada da tsaffin gwamnoni, mataimakan gwamnoni, shugabannin majalisar dattawa, da sauran manyan jami’ai daga sassan siyasa da shari’a na jihar.

Dawakin Tofa ya yi nuni da cewa jihar ta tana dimbin dattawa da tsofaffin shugabanni da suka samu nasarar gudanar da ayyukansu da kuma ci gaba da kasancewa cikin koshin lafiya.

 Daga cikin fitattun mutanen da majalisar ta kunsa akwai tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, wanda a halin yanzu yake rike da mukamin shugaban jam’iyyar APC.  Majalisar za ta kuma kunshi alkalan kotun koli da na daukaka kara da suka yi ritaya da kuma tsoffin alkalan jihar da sakatarorin gwamnatin jihar da kuma shugabannin ma’aikatan gwamnati wadanda dukkansu ‘yan asalin jihar Kano ne.

 Sannan majalisar za ta samu jagorancin Malamai (malaman addini), ’yan kasuwa, sarakunan gargajiya, da tsaffin shugabannin hukumomin tsaro daga jihar Kano.  Sanarwar ta kara da cewa gwamnati za ta tantance tare da nada wasu fitattun dattawan da za su jagoranci majalisar.

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *