KanunLabarai

Golan Man Utd Onana Ya fusata Bayan  an Ajishi a Benhci a wasan Kamaru na farko a gasar AFC

Rahotanni sun ce Andre Onana ya fusata ne bayan da ya dauki jirgin sama mai zaman kansa domin buga wasan farko na AFCON da Kamaru amma kocin bai saka shi ba.

Andre Onana ya kwashe ‘yan mintoci na karshe a Manchester don taimakawa kungiyar Ten Hag a wasan da suka tashi 2-2 da Tottenham a Old Trafford.

 Bayan wasan, mai tsaron gidan Red Devils ya dauki jirgin sama mai zaman kansa don tashi zuwa gabar tekun Ivory Coast domin bude gasar AFCON ta tawagar kasarsa ta Kamaru.

 Duk da wannan yunƙuri da isowar sa’o’i kaɗan kafin wasan, kocin bai zaɓe golan Kamaru ba don wasan tsakanin Kamaru da Guinea.

 Rahotanni sun bayyana cewa tsohon dan wasan Senegal El Hadji Diouf dole ne ya kwantar wa da golan Manchester United Onana hankali lokacin da ya fahimci cewa an cire shi daga cikin ‘yan wasan da za su fafata.

 “Idan ba zan buga wasa ba ko kuma in yi kungiyar, me yasa na zo nan a jirgin sama mai zaman kansa?” Abin da Onana ya yi ihu a fusace.

Domin cigaba da samun sahihan labarai Masu Ilimantarwa da fadakarwa harma da nisha dan tarwa shiga group na WhatsApp na labarangriyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Facebook page:

https://www.facebook.com/profile.php?id=61555682938654&mibextid=9R9pXO

Twitter / X

https://x.com/gariyawaye01?t=u5eyTeHjmBbA2fuehmGMPQ&s=09

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *