KanunLabarai

Gwamna Ganduje Ya Gayyaci Gwamnan Kano Zuwa APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci gwamna Abba Kabir Yusuf da ya yi watsi da jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) zuwa APC.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron masu ruwa da tsaki a Kano, Ganduje ya ce taron ya yanke shawarar bude kofofin APC ga sauran masu son shiga jam’iyya mai mulki.

“Muna kira ga masu son komawa APC su zo. Musamman muna gayyatar Gwamnan Kano da jam’iyyarsa ta NNPP zuwa APC,” inji Ganduje.

Shugaban jam’iyyar na kasa ya roki ‘yan jam’iyyar da kada su karaya a kan asarar karar zaben gwamna da aka yi a kotun koli.

Ya ce a matsayinsu na masu bin tafarkin dimokaradiyya, ya kamata mambobin su gode wa Allah.

Wasu Sanatoci da ‘Yan Majalisar Wakilai, Ganduje ya ce sun koma APC, inda ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba wasu gwamnonin za su sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki.

Ya ce Tinubu na son Kano kuma ya dage cewa jihar ta samar da mataimakin shugaban majalisar dattawa duk da matsananciyar matsin lamba.

Dukkan tsaffin kwamishinoni da shugaban ma’aikatan da suka yi aiki a karkashin Ganduje sun halarci taron.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *