KanunLabarai

Iftilain Gobara: Mai Gida, Mata da Yara 5 Sun Mutu.

A cewar wani jami’in hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullah ya dora alhakin faruwar gobarar da ta lakume gidajen wasu ‘yan uwa guda bakwai tare da masallacin Juma’a na Tudun Wada a cikin tsohon gari, akan wutar lantarki.

 Abdullahi ya ce hukumar kashe gobara ta samu kiran gaggawa a ofishin kashe gobara dake Dakata daga wani Ibrahim Sani da misalin karfe 12:25 cikin dare, cewa gobara ta tashi a wani gini da ke Unguwar Tudun Wada Birget.

“Da samun labarin, mun aika da motar kashe gobara zuwa wurin da misalin karfe 12:30am,” in ji shi.

 Ya ce jami’an kwana-kwana sun kwashe mutane bakwai da suka suma daga cikin dakuna biyu da suka kone kadan, aka garzaya da su asibiti.

“Likitan ya tabbatar da mutuwar bakwai daga cikin su sakamakon hayakin da suka shaka,” in ji shi, ya kara da cewa bincike ya nuna cewa wutar lantarkirar ce ta haifar da gobarar, kuma wutar tayi karfi kafin isar jami’an kwanakwana.

Ya shawarci jama’a da su yi taka-tsan-tsan a yayin da ake sarrafa na’urorin lantarki da abubuwan da za su iya cin wuta don guje wa afkuwar gobara da sauran abubuwan gaggawa.

(NAN)

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *