LABARAI DA DUMI-DUMIN SU: (Zaben Cike gurbi): INEC Ta Dakatar Da Sake Zabe a Jahohi Uku.
GARI YA WAYE ta rawaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta dakatar da sake gudanar da zabe a mazabu uku: Enugu ta Kudu 1 (jihar Enugu), Ikono/Ini (jihar Akwa Ibom), da Kunchi/Tsanyawa (jihar Kano). Dalilin dakatar da zaben dai shi ne tashe-tashen hankula, rashin bin ka’ida, da kuma sace jami’an zabe….