KanunLabarai

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU: (Zaben Cike gurbi): INEC Ta Dakatar Da Sake Zabe a Jahohi Uku.

GARI YA WAYE ta rawaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta dakatar da sake gudanar da zabe a mazabu uku: Enugu ta Kudu 1 (jihar Enugu), Ikono/Ini (jihar Akwa Ibom), da Kunchi/Tsanyawa (jihar Kano).

Dalilin dakatar da zaben dai shi ne tashe-tashen hankula, rashin bin ka’ida, da kuma sace jami’an zabe. Wannan yana nuna damuwa game da gaskiya da amincin tsarin zaɓe.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin kwamishinan INEC na kasa & shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe, Sam Olumekun.

Wakilinmu ya kuma tattaro cewa a mazabar Kunchi/Tsanyawa na jihar Kano, an samu cikas a harkokin gudanar da zabe a karamar hukumar Kunchi da suka hada da rumfunan zabe 10.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *