KanunLabarai

Takaitattun Labaran Duniya 07/07/1445AH – 19/01/2024CEG

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta mayar da shalkwatar hukumar kula da filayen jiragen saman ƙasar (FAAN) zuwa birnin Lagos.

Rundunar yan sanda ta jihar Bauchi ta kama wani dalibin aji 4 a Jami’ar Tafawa Balewa ta Bauchi (ATBU), Mike James Habila dauke da bindigu.

Kotun ƙoli zata yanke hukunci kan kararrakin da aka kalubalanci nasarar gwamnonin jihohi biyar a yau juma’a a jihohin Ogun, Delta, Nasarawa, Kebbi da kuma jihar Gombe.

’Yan bindiga sun tarwatsa al’ummar kauyuka 10 da ke zaune a yankin Kidandan na Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Shugaba Tinubu, ya gana da shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Kano a fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock da ke Abuja.

Kotu ta bayar da umarnin kama Dakta Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi. 

Gwamnatin Abba a jihar Kano ta fara rabon tallafin kayan abinci ga ma’aikatan kananan hukumomi don rage radadin janye tallafin man fetur. 

An yi musayar wuta mai zafi, a ranar Alhamis, yayin da ‘yan sanda suka kubutar da Segun Akinyemi, wani mazaunin Abuja, tare da kama wasu daga cikin ‘yan bindigar. 

Hukumar Zabe ta Jihar Gombe, ta ayyana 27 ga watan Afrilun 2024 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar.

Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya tube rawanin wasu sarakunan gargajiya uku. 

Gwamnan jihar Abia Alex Otti ya nada mai girma Muhammadu Sanusi II, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala da wasu a matsayin mambobin cibiyar tattalin arzikin jihar. 

Dakarun rundunar  Sojoji tare da haɗin gwiwar ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa a jihar Benue. 

Wani bam da aka dasa a amalanken Jaki ya kashe ɗan sanda a Kenya. 

EU da Amurka sun bayyana damuwa a kan rikicin Pakistan da Iran. 

Gwamnatin Nijar ta soke tsarin sake bai wa ma’aikatan da suka yi ritaya aiki. 

Wasanni

  • Copa Del Rey: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Real Madrid da ci 4:2 a wasan jiya.
  • Copa Del Rey: Barcelona ta sami nasara akan Salamanca da ci 3:1 a wasan jiya. 
  • AFCON: Nigeria ta sami nasara akan Ivory Coast da ci 1:0 a wasan jiya. 
  • AFCON: Equatorial Guinea ta sami nasara akan Guinea Bissau da ci 4:2 a wasan jiya. 
  • AFCON: Ghana da Egypt sun tashi 2:2 a wasan jiya.
Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *