Yan sanda a jihar Kogi sun kama wata mata da ta jefa jaririyarta mai watanni biyar a duniya a cikin kogi da nufin kashe ta.
Wata gobara da ba a gano musabbanin tashinta ba ta kona shaguna fiye da 450, da gidajen abinci 5, hadi da otel 2 a rukunin shagunan Mandola da ke Jihar Legas.
’Yan majalisar Filato da kotu ta kwace kujerunsu sun lashi takobin dowawa bakin aiki.
Shugabannin APC sun zargi ‘Yan Kwankwasiyya da shiga rigar jam’iyya domin ganin bayan Dr. Abdullahi Ganduje.
‘Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 16 a wani hari da suka kai kauyen Tsohon Dungunu da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.
Ƙanin mahaifin su Nabeeha da Yan bindiga suka sakil ya shaida wa BBC cewa ƴan’uwa ne suka biya kuɗin fansa ga ƴan bindigar don a sake su ba kamar yadda ƴan sanda suka yi iƙirarin cewa su ne suka kuɓutar da su ba.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke kasafin kudin Jihar Ribas na Naira biliyan 800 na shekarar 2024 da Gwamna Siminalayi Fubara ya gabatar.
Sanatar Abuja, Ireti Kingibe, ta zargi Ministan Birnin, Nyesom Wike da kin sauraron ta domin tattaunawa kan matsalar tsaro da ke ci wa birnin tuwo a kwarya.
Wani abu ya fashe a wata makarantar Islamiyya, inda dalibi daya ya rasu, sannan wasu 10 suka jikkata a kauyen Kidandan da ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Hukumar Zabe ta Jihar Gombe, GOSIEC, ta ayyana 27 ga watan Afrilun 2024 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar.
Gwamnatin Legas za ta sa takunkumi kan masu magungunan gargajiya.
Mutun takwas sun mutu, 47 sun bace bayan zaftarewar kasa a China.
Sakataren Kasashen Wajen Amurka, Antony Blinken ya fara ziyarar kasashen Yammacin Afrika da Sahel.
Sabon shugaban Laberiya ya kusa shiɗewa a lokacin shan rantsuwa.
Yan sandan Kenya sun gano kokon kan wata daliba da aka yi wa kisan gilla.
Kusan mutum 90 sun mutu sanadin muku-mukun sanyi a Amurka.