KanunLabarai

Takaitattun Labaran Duniya 

 • Yan sanda a jihar Kogi sun kama wata mata da ta jefa jaririyarta mai watanni biyar a duniya a cikin kogi da nufin kashe ta.
 • Wata gobara da ba a gano musabbanin tashinta ba ta kona shaguna fiye da 450, da gidajen abinci 5, hadi da otel 2 a rukunin shagunan Mandola da ke Jihar Legas.
 • ’Yan majalisar Filato da kotu ta kwace kujerunsu sun lashi takobin dowawa bakin aiki.
 • Shugabannin APC sun zargi ‘Yan Kwankwasiyya da shiga rigar jam’iyya domin ganin bayan Dr. Abdullahi Ganduje.
 • ‘Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin garkuwa da wasu 16 a wani hari da suka kai kauyen Tsohon Dungunu da ke karamar hukumar Munya a jihar Neja.
 • Ƙanin mahaifin su Nabeeha da Yan bindiga suka sakil ya shaida wa BBC cewa ƴan’uwa ne suka biya kuɗin fansa ga ƴan bindigar don a sake su ba kamar yadda ƴan sanda suka yi iƙirarin cewa su ne suka kuɓutar da su ba.
 • Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke kasafin kudin Jihar Ribas na Naira biliyan 800 na shekarar 2024 da Gwamna Siminalayi Fubara ya gabatar.
 • Sanatar Abuja, Ireti Kingibe, ta zargi Ministan Birnin, Nyesom Wike da kin sauraron ta domin tattaunawa kan matsalar tsaro da ke ci wa birnin tuwo a kwarya.
 • Wani abu ya fashe a wata makarantar Islamiyya, inda dalibi daya ya rasu, sannan wasu 10 suka jikkata a kauyen Kidandan da ke Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
 • Hukumar Zabe ta Jihar Gombe, GOSIEC, ta ayyana 27 ga watan Afrilun 2024 a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar.
 • Gwamnatin Legas za ta sa takunkumi kan masu magungunan gargajiya.
 • Mutun takwas sun mutu, 47 sun bace bayan zaftarewar kasa a China.
 • Sakataren Kasashen Wajen Amurka, Antony Blinken ya fara ziyarar kasashen Yammacin Afrika da Sahel.
 • Sabon shugaban Laberiya ya kusa shiɗewa a lokacin shan rantsuwa.
 • Yan sandan Kenya sun gano kokon kan wata daliba da aka yi wa kisan gilla.
 • Kusan mutum 90 sun mutu sanadin muku-mukun sanyi a Amurka.
Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *