KanunLabarai

Takaitattun Labaran Duniya

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya sabonta nadin Bayero Farah a matsayin shugaban Hukumar Koyar Da Fasahar Sufuri a Najeriya (NITT).
  • Tsofaffin sojoji sunce ana bukatar hadin kai daga sauran jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da matasa domn magance matsalar tsaro a Najeriya
  • Hedikwatar tsaro ta ce dakarun sojin Najeriya sun halaka wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ƴan ta’addan ISWAP guda uku a Borno.
  • Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya ce ba shi da sha’awar sake neman wani muƙamin siyasa bayan ya kammala wa’adinsa na 2 a matsayin gwamna.
  • Yan bindiga sun kashe shugaban makarantar sakandare (GSS) Kuriga, karamar hukumar Chukun da ke jihar Kaduna.
  • ‘Yan bindiga sanye da hijabi sun sake afka wa jami’an tsaro a yankin Batsari, sun kashe ‘yan sandan Mofal biyu.
  • Shahararriyar mawakiyar Najeriya, Tiwa Savage ta gamu da ‘yan kwanta-kwanta a birnin Landan da suka yi mata fashi da makami.
  • Masu garkuwa da mutane sun bude wuta wa wani mai suna Abdullahi Sabo a hanyar sa ta komawa gida da matar sa a Abuja.
  • Najeriya:’Yan bindiga sun kashe mutane 4 har da sojoji a jihar Benue.
  • Kungiyar AU ta naɗa Obasanjo, ya jagoranci tattaunawar shiga tsakani kan rikicin Somalia da Ethgiopia.
  • An kashe dakarun juyin-juya halin Iran a wani hari da ake zargin Isra’ila ta kai Siriya.
  • Mutum 13 sun mutu a wata gobara da ta tashi a makarantar yara a China.
  • Hadaddiyar Daular Larabawa ta dauki nauyin ginawa Afirka ta Tsakiya sabon filin jirgin na zamani.
  • AFCON: Dan wasan gaban Masar Mohamed Salah zai yi jinyar da za ta hana shi buga wasanni 2 na gaba a gasar sakamakon raunin da ya ji a cinyarsa.
  • EPL: Arsenal ta sami nasara akan Crystal Palace da ci 5:0 a wasan yau.
  • AFCON: Algeria da Burkina Faso sun tashi 2:2 a wasan yau.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *