Wata Kotun majistire mai Lamba 32, dake zaman ta a Norman’Sland dake unguwar Sabon gari dake Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Abdul’aziz Habib, ta bayar da belin Danbilki Kwamanda.
Tunda farko ana zargin Danbilki Kwamanda, da laifin furta wasu kalamai da za su iya haifar da tunzuri ga al’umma, musamman kan abunda ya shafi masarautun jahar Kano guda biyar.
Sharudan Belin da kotun ta gidanya wa, Ɗanbilki Kwamanda sun hada da mutane biyu da za su tsaya masa, wajibi ne kuma daya daga cikinsu ya zama babban sakataren gwamnatin jahar Kano da kuma Hakimi.
Kuma sannan zasu a ajiye kudi naira miliyan daya da hotunan su harda na wanda ake zargin.
Mai shari’a malam Abdul’aziz Habib ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Fabarairun 2024 , don ci gaba da sauraren shari’ar.
Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye
https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx
Torawa Yan'uwa Da Abokai