KanunLabarai

An Daskarar da asusun bankin Hisbah saboda karar Wasu Masu Otal a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce an rufe dukkan asusun ajiyarta na banki biyo bayan karar da masu otal a jihar suka yi wa hukumar.

Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya tabbatarwa da tashar TRT Afrika Hausa a ranar Laraba.

A ‘yan watannin da suka gabata, wani samame da hukumar Hisbah ta kai wasu otal-otal da wuraren shakatawa a Kano ya haifar da cece-kuce.

Daurawa ya ce, “Eh, gaskiya duk an kulle asusun bankin mu. Na aika da wakili ya gana da babban lauya saboda ba a fada mana laifin da ake zargin mu akaiba da kuma dalilin rufe asusun ba.

“Mun samu takardar kotu da ke nuna rashin da’a a wasu otal guda biyu, wanda hakan ya sanya aka tuhume mu akan Chaji na N700,000 da N100,000. Takardar ta bukaci a hada su a biya su Naira 800,000 wanda hakan ya sa aka rufe asusun mu.

“Ya kamata a gaya mana laifin da muka aikata domin mu nemi lauyoyinmu su shiga cikin tattaunawar. Idan muka kasa kare kanmu, to za a hukunta mu.”

Daurawa ya kuma nuna damuwarsa kan yadda hukuncin da kotun ta yanke ya gurgunta ayyukan Hisbah saboda kulle asusun ajiyar bankin.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *