KanunLabarai

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Jiha Ta Bayyar Da Hutu Ranar Laraba Ga Ma’aikatan jihar

DA DUMI-DUMI: Gwamnatin Jiha Ta Bayyar Da Hutu Ranar Laraba Ga Ma’aikatan jihar

GARI YA WAYE ta rawaito cewa Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ayyana ranar Laraba 7 ga watan Fabrairun 2024 a matsayin ranar kyauta ta aiki domin gudanar da addu’o’in kwanaki uku ga marigayi tsohon gwamnan jihar, Sen. Bukar Abba Ibrahim.

Buni, wanda ya bayyana hakan a ranar Talata cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mamman Mohammed ya fitar, ya ce a yi amfani da wannan rana wajen yin addu’a ga tsohon gwamnan da ya rasu a kasar Saudiyya ranar Lahadi.

Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa marigayin addu’ar samun rahama.

Za a gudanar da addu’o’in kwanaki uku ga marigayi tsohon gwamnan da ya rasu kuma aka binne shi a kasa mai tsarki a masallacin gidan gwamnati dake Damaturu.

Gwamnatin jihar Yobe ta dauki nauyin gudanar da jana’izar da ta’aziyya a hukumance, domin karrama marigayi gwamnan.

Buni, tare da jami’an gwamnati da iyalan marigayi gwamnan, suna ta samun ta’aziyya daga ciki da wajen jihar a fadar gwamnati dake Damaturu.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *