KanunLabarai

Shugaba Tinubu Ya Koma Abuja Bayan Ziyarar Sirri Ta Sati Biyu A Kasar Faransa

GARI YA WAYE ta ruwaito cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan ya shafe makonni biyu yana jinya a kasar Faransa.

In zamu iya tunawa cewa Tinubu a ranar Laraba 24 ga watan Janairu ya bar Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a wata ziyarar sirri.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar, an shirya shugaba Tinubu zai dawo kasar ne a makon farko na watan Fabrairu, 2024.

‘yan Najeriya suna yin hasashe. Shugaban kasar zai magance tsadar rayuwa a kasar, rashin tsaro da dai sauran su, yanzu da ya dawo daga tafiyarsa,

Ziyarar karshe da Tinubu ya yi zuwa kasar nan ita ce halartar taron sauyin yanayi karo na 28 na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya gudana a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a watan Disambar bara.

Baya ga halartar taron da aka yi a Dubai, shugaban ya gana da Sarki Charles na Ingila, da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa, da shugabannin kasashe da dama da abokan huldar bangarori daban-daban domin cimma matsaya.

Tinubu ya kuma shaida rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai cike da ci gaba tsakanin Najeriya da Jamus don inganta wutar lantarkin Najeriya tare da gudanar da wani babban taro tare da masu ruwa da tsaki da masu zuba jari kan Kasuwar Carbon Najeriya da shirin kaddamar da motocin bas na lantarki a gefen taron yanayi na COP28.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *