KanunLabarai

DA DUMI-DUMI: Wani Sanata mai ci ya tsallake rijiya da baya a Imo, an kashe mai tsaron sa wato (orderly)

Gari ya waye ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan Sanata mai wakiltar Imo-North Senatorial District (Okigwe zone), Sanata Patrick Ndubueze, wanda ya yi sanadin mutuwar daya daga cikin mai tsaronsa sa.

Wata majiya da ke kusa da Sanatan ta shaida wa majiyarmu ta kasa cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Sanatan ne a safiyar ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu.

Majiyar ta kara da cewa yayin da Sanatan ya yi nasarar tserewa ba tare da ya samu rauni ba, an harbe daya daga cikin ‘yan sandan da aka nada shi har lahira.

Ya ce: “Labarin da aka kai wa Sanata Patrick Ndubueze gaskiya ne. Sun kai farmaki gidansa da ke Umualumoke inda suka kashe wani dan sanda da ke yi masa aiki.

“Sun mamaye gidansa kuma an bindige daya daga cikin ‘yan sandansa a cikin lamarin. Kazalika wasu ‘yan barandan ne suma suka yi wa hukumar gidan yari kwanton bauna a Okigwe tare da ‘yantar da fursunoni bayan kashe wani sifeton ‘yan sanda tare da sace jami’in da ke kula da cibiyar.

“Okigwe ya zama yankin yaki da babu wanda ya tsira. Muna rayuwa cikin tsoro gaba ɗaya. Galibin matasan mu sun gudu ne saboda tsoron kada a kashe su. Hukumomin tsaron mu ba sa yin abin da ya dace wajen yaki da miyagun laifuka a jihar. Amma duk da haka, akwai da yawa daga cikinsu (ma’aikatan tsaro) a wannan yanki,” in ji shi.

A halin yanzu dai Sanata Patrick Ndubueze  dan majalisar dattawa ne a jam’iyyar APC wanda ya lashe zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo, Henry Okoye, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aboki Danjuma ya kafa wata tawagar da za ta bi bayan maharan.

Domin samun Sahihan labarai da dumi-dumin su. Latsa wannan link 👇🏻👇🏻👇🏻

https://t.me/labarangariyawaye

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *