KanunLabarai

DA DUMI-DUMINSA: An Yi Zanga-zanga A Minna Kan tsadar Rayuwa A Najeriya

Rahotanni dake fitowa daga jahar Neja na cewa a ranar Litinin ne mazauna garin Minna, babban birnin jihar Neja, suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a kasar, tare da toshe manyan tituna a cikin birnin.

An ji masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa suna rera wakokin zanga-zangar, yayin da jami’an tsaro ciki har da ‘yan sanda suka sa ido akan masu zanga-zangar.

Masu zanga-zangar sun ce tsadar kayan abinci da kuma rashin kokarin da gwamnati ke yi na kame lamarin ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.

Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba, a lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zangar, ya ce gwamnati na sane da kuncin rayuwa da iyalai ke fuskanta a wannan lokaci.

Ya ce gwamnati na kokarin rage tsadar rayuwa da sakamakon cire tallafin man fetur ya jawo.

Karin bayani na tafe………

 

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Facebook page:

https://www.facebook.com/profile.php?id=61555682938654&mibextid=9R9pXO

X page:

https://x.com/gariyawaye01?t=iPkME2Ddq50H0i5Qf20phw&s=09

 

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *