KanunLabarai

‘Yan bindiga sun bukaci a biya su Naira miliyan 40 domin su sako matar wani basaraken gargajiya da aka kashe a jihar Kwara

‘Yan bindigar da suka kashe wani basaraken gargajiya, suka yi garkuwa da matarsa da wani mutum guda, sun rage kudin fansa zuwa Naira miliyan 40 daga Naira miliyan 100.

A ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan bindigar suka kai wa iyalan sarkin kudin fansa Naira miliyan 100.

An kashe basaraken gargajiya, Oba Olusegun Aremu-Cole, wanda shi ne Olukoro na Koro-Ekiti a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara, a fadarsa da daddare.

A lokaci guda maharan sun yi awon gaba da matarsa da wani mutum guda.

Da yake magana da manema labarai a yammacin ranar Lahadi, Mista Kehinde Bayode, shugaban kwamitin aiwatar da mulki (TIC) a karamar hukumar Ekiti ta jihar Kwara, ya kuma ce an kama wani da ake zargi.

Yayin da yake magana kan kokarin da aka yi na kubutar da matar sarkin da aka yi garkuwa da ita da kuma wani mutum, Bayode ya ce: “Masu garkuwa da mutanen sun samu tattaunawa da iyalan.

“Suna neman kudin fansa nera miliyan 100, wanda a yanzu an mayar da shi Naira miliyan 40.

“Amma har yanzu muna tattaunawa da su, kuma a yanzu haka, ina kan hanyara ta zuwa Koro don samun sabbin bayanai kan tattaunawar.

“Za mu ci gaba da yi muku bayani (‘yan jarida) yayin da lamarin ke faruwa, kuma za mu ci gaba da sanar da ku,” in ji shi da yammacin ranar Lahadi.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi, bai tabbatar da kama wani da ake zargi ba.

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *