KanunLabarai

Gwamnatin Najeriya ta Ƙaddamar da hukumar kula da Almajirai da sauran Yaran da basa zuwa Makaranta.

Gwamnatin Najeriya ta Ƙaddamar da hukumar kula da Almajirai har ma da sauran Yaran da basa zuwa Makaranta.

Mai girma Ministan ilimin Najeriya Farfesa Tahir Mamman ya Jagoranci Ƙaddamar da Hukumar,  ya kara jaddada aniyar Gwamnatin na ci-gaba da inganta ilimin Yara kanana a fadin kasar.

Ministan ilimin ya cigaba da cewa, Ƙaddamar da hukumar a gwamnatance na a matsayin ɗamba, da gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaban kasar Bola Tinubu ta sanya wajen ceto rayuwar dumbin Yara dake watangaririya, musamman a kan titunan birane kasar.

Hon Sha’aban Sharada shine Shugaban Sabuwar hukumar, ya ce zata rinƙa sanya idanu tare da inganta rayuwar almajirai da Yaran da basa zuwa Makaranta.

Inda ya ƙara da cewa tuni suka fitar da tsarin yadda zasu tafiyar da aikin hukumar domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu

Anata bangaren, Mai dakin Ministan kasafi da tsare-tsare na Najeriya kana Shugabar Gidauniyar malpai dake bada agaji ga masu karamin karfi da masu bukata ta musamman, Hajiya Aisha Atiku Bagudu tace gidauniyarta zata yi aiki kafada da kafada da sabuwar hukumar domin ganin haka ta cimma ruwa.

A yayin taron, Mamba a Majalisar wakilan Najeriya ta goma kana Wanda ya ɗauki gaɓarar gabatar da wannan kudiri gabanin ya zama doka a zamanin Majalisa ta Tara da ta gabata, Hon Dakta Balarabe shehu kakale ya bayyana farincikinsa dangane da kaddamar da wannan hukuma.

A ƙarshe Dakta Balarabe ya Miƙa godiyar sa ga dukkan waɗanda suka tallafa wajen tabbatuwar hukumar, tare da fatan hukumar zata zama silar canza Rayuwar yaran Najeriya

Idongari.ng

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *