KanunLabarai

Ibtilai: Yan Bindiga sun sake sace wasu ‘yan mata ‘yan gida daya a Abuja

Photo credits: VOA News

Wasu ‘yan bindiga su shida sun far wa wani gida a kauyen Guita da ke Chikakore, a yankin Kubwa da ke Abuja inda suka yi awon gaba da ‘yan mata guda biyu ‘yan uwan juna masu shekaru 16 da 14.

Bayan kwashe ‘yan matan ne kuma ‘yan bindigar suka ranta a na kare inda suka shiga daji wanda ya hada kauyen da wasu kauyukan masu makwabtaka.

Wani shaida ya fada wa jaridar Daily Trust cewa ” la ranar Lahadi lokacin da ‘yan bindigar suka je sun kutsa gidan ne ba tare da harbi irin na kan-mai-uwa-da-wabi ba kamar yadda suka saba sannan suka kama ‘yan matan guda biyu.”

Wannan ne dai karo na biyu a kasa da wata guda da ‘yan bindiga ke yin garkuwa da ‘yan mata ‘yan uwan juna a babban birnin na tarayya.

Batun tsaro na kara ta’azzara a birnin na Abuja wani abu da ke kara jefa fargaba a zukatan mazauna birnin.

To sai dai a baya rundunar ‘yan sandan birnin ta sha cewa tana iya bakin kokarinta wajen ganin su dakile matsalar.

Idongari

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *