KanunLabarai

KWAMISHINAN ILIMI YA DAKATAR DA ALBASHIN MALAMAN WATA MAKARANTAR SAKANDIRE NAN TAKE.

Kwamishinan ya bada umarnin dakatar da albashin malaman GSS Gabasawa nan take

Mai girma kwamishinan ilimin jahar Kano, Hon Umar Haruna Doguwa yakai ziyarar bazata zuwa makarantar GSS Gabasawa a wannan safiya ta litinin 5/01/2024.

Da misalin karfe 8:45am mai girma kwamishinan ilimi yakai ziyara amma malamai 5 kawai ya samu a makarantar, nan take ya bada umarnin tsaida albashin dukkan malaman da basu zo ba sannan da Query wato (tuhuma).

Wanan sanarwa ce daga Mai magana da yawun Kwamishinan Ilimi na Jahar kano Abba Rabi’u Gwarzo .

Abaya dai Kwamishinan Ilimi na Jahar kano ya sha jan hankalin ma’aikatan dake aiki a karkashin ma’aikatar ilimi akan zuwa wajen aiki da tashi akan lokaci.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *