KanunLabarai

Mun Kama ‘Yan dabar da Wani Dan Siyasa ya tura ƙunci da Tsanyawa – CP Gumel.

Photo credits: idongari.ng

Rundunar ‘yan Sandan Kano ta tabbatar da kama wasu ‘yan Daba, da ake zargin wani Dan Siyasa ya tura wurin Zaɓen cike gurbi ,na ƙananan Hukumomin ƙunci da Tsanyawa.

Kwamishinan ‘Yan Sandan kano CP. Muhammad Hussaini Gumel ne ya bayyana hakan, Jim kadan da kama gungun matasan a lokacin da suke zagayen yadda Zaɓen cike gurbin yake gudana.

CP Gumel ya ƙara da cewa, tuni ‘Yan daban suka kama sunan ɗan Siyasa me Suna Gwarmai, a matsayin Wanda ya turo su domin su je su tayar da hankali a wurin Zaɓen cike gurbin na Ƙunci da Tsanyawa.

Yan Sandan sun kama ‘yan dabar da makamai ne, samfurin Adduna, Gorori, Gariyo, da dai sauran su, a dai-dai lokacin da suke kan hanyar su ta shiga garin Ƙunci.

“Gumel yace zasu Binciki Dan Siyasar domin tabbatar da gaskiyar lamarin dama gurfanar dashi a gaban kuliya, matukar zargin yayi ƙarfi a kansa”.

Latsa wannan link domin kallo da sauraren C.P GUMEL 👇👇👇👇👇

Bidiyon Yadda aka kama Yan dabar

Daga: Idongari.ng

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *