KanunLabarai

Takaitattun Labaran Safiyar Asabar 22/07/1445AH – 03/02/2024CE

  • Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya bukaci shugaba Tinubu da ya rufe idonsa ya dauki kwararan matakai kan mukarrabansa da suka kasa gudanar da ayyukan da ke wuyayensu.
  • INEC za ta gudanar da zaɓukan raba gardama da kuma na cike gurbi na kujerun majalisun tarayya da kuma na jihohi a faɗin jihohi 26 a yau Asabar.
  • Gwamnati ta danganta ƙara taɓarɓarwar wutar lantarki a ƙasar nan da dalilan rashin samun wadataccen gas ga kamfanonin samar da wuta wato, GenCos.
  • Gwamnatin jihar Oyo ta rufe coci saboda damun maƙwabta da hayaniya.
  • Olayemi Cardoso ya amince an saki $500m domin biyan bashin kudin waje da ake bin CBN a Najeriya.
  • Rundunonin ‘yan sanda sun ce za su takaita zirga zirga a wasu yankuna a yayin da INEC ke gudanar da zabukan cike gurbi a jihohi 26 na Nijeriya ranar Asabar.
  • Atiku Abubakr yace Kuskure ne shugaba Tinubu ya ce CBN ya karbe kudaden cinikin da NNPC ke yi
  • Manoma dubu 36 za su ci gajiyar shirin noman Fadama na GO-CARES a Gombe.
  • Sanata Elisha Abbo ya zargi shugabar kotun daukaka kara, Monica Dongban-Mensen da karbar cin hanci.
  • ‘Yan bindiga sun sace mata kusan 55 yan raka amarya har ɗakin aurenta a titin zuwa Damari, karamar hukumar Sabuwa a Katsina.
  • Kotun majalisar dinkin duniya ta ce tana da hurumin sauraron shari’ar Ukrane da Rasha.
  • AFCON: Nigeria ta tsallaka semi final bayan samun nasara akan Angola da ci 1:0 a wasan jiya.
  • AFCON: Congo ta tsallaka semi final bayan samun nasara akan Guinea da ci 3:1 a wasan jiya.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *