KanunLabarai

Tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi ya jaddada goyon bayan manufofin tattalin arzikin Tinubu, Yace Gwamnatin Baya ce ta jawo wahalhalu a Najeriya

Photo credits: intelregion.ng

Tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi, ya jaddada goyon bayansa ga  tattalin arziki na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. yana mai cewa rashin adalci ne a dora wa gwamnatinsa a kan matsalar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

Sanusi ya ce kasar na fama da tabarbarewar tattalin arziki sakamakon rashin gudanar da manufofin tattalin arziki na shekaru takwas da suka gabata.

Da yake magana a ranar Lahadin da ta gabata yayin wani taron addini, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, ya ce gwamnatin Buhari ta gaza bin shawararsa kan yadda za a ceto kasar daga matsalolin tattalin arziki.

Ya ce ba zai bi sahun masu rajin sukar Tinubu kan kalubalen tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu ba.

Tsohon gwamnan, babban bankin Najeriya, ya sha alwashin sukar Tinubu idan ya ga wata manufar tattalin arzikin da ba ta dace ba a nan gaba.

Sanusi ya ce, “Na shafe shekaru ina magana a kan rikicin da ake ta fama da shi kafin tabarbarewar tattalin arziki. Duk wani masanin tattalin arziki da ya yi nazarin manufofin kudi a cikin shekaru takwas da suka wuce ya san cewa ‘yan Najeriya za su fada cikin wannan mawuyacin hali.

“Matsalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta shi ne mafari  (idan ba a yanke shawarar da ta dace ba) domin Najeriya ba ta da wani yanayi; irin wannan yanayi ya faru a Jamus, Zimbabwe, Uganda, da Venezuela.

“Gwamnatin da ta shude ta bijire kan kiran da muka yi na neman gyara (a tsarin tattalin arziki). Na ce a gaban shugaban kasa mai ci yanzu a jihar Kaduna, duk dan siyasar da ya ce maka abu zai yi sauki, kada ka zabe shi domin karya yake yi. Mutane sun yi watsi da shawara ta a matsayin sanarwa ta siyasa.

“Idan zan yi adalci kuma in yi wa Shugaba Bola Tinubu adalci, ba shi ne ya jawo wahalhalun da ake ciki a yanzu ba; tsawon shekaru takwas, muna rayuwar karya tare da bashi mai yawa daga basusukan waje da na cikin gida. Babban Bankin Najeriya na bin bashin sama da Naira Tiriliyan 30, wanda hakan ya sa bashin ya haura kashi 100 cikin 100.

“Ba zan iya shiga cikin wasu ‘yan Najeriya da ke sukar Tinubu kan matsalar tattalin arziki da ake ciki a halin yanzu ba, kuma ba wai ina cewa shi waliyyi ne da ya kubuta daga aikata ba daidai ba, amma a halin da ake ciki na tattalin arzikin da ake ciki, ba za a zargi Shugaba Tinubu ba. Zan kuma yi magana idan na ga wata manufar tattalin arziki mara kyau na gwamnatin Tinubu a nan gaba, in ji.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *