Sanata Adams Oshiomhole ya tabbatar da cewa babu zaman lafiya ga kowace gwamnati ko a jiha ko karamar hukuma da ta gaza aiwatar da tallafin N35,000 na Gwamnatin Tarayya.
“Gwamnatin tarayya ta amince da karin Naira 35,000 a kan albashin ma’aikata. Amma har yanzu ban fahimci dalilin da ya sa babu wata gwamnati a Najeriya ko gwamna da ya aiwatar da wannan yarjejeniya,” Oshiomhole ya bayyana haka yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.
Ya kuma jaddada cewa ya kamata a aiwatar da bayar da kyautar albashi na wucin gadi a dukkan matakai na gwamnati har ma a kai ga kamfanoni masu zaman kansu.
“Ban yarda cewa kudin na ma’aikatan tarayya ne kawai ba. Ma’aikatan tarayya ba su da kasuwanni daban-daban da ma’aikatan Jihohi da kuma gwagwarmayar da aka yi, ma’aikata a Najeriya an hada su da ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu abin da muka kira yajin aikin gama-gari kafin a ba da wannan kudi,”.
Oshiomhole ya jaddada cewa aiwatar da karin albashin N35,000 ya kamata ya zama wani aiki na kasa baki daya, inda ya bukaci kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da ma’aikata su matsa kaimi wajen aiwatar da shi.
“Saboda haka, ya kamata dukkan gwamnatocin jihohi, kananan hukumomi, gwamnatin tarayya, da ma’aikata masu zaman kansu su aiwatar da shi. Ba na tunanin NLC zatayi kasuwanci da hakkin ma’aikata . Kamata ya yi su yi gwagwarmaya domin kwato musu hakkinsu,” in ji shi.
A karshe ya bayyana ra’ayinsa karara: “Duk gwamnatin da ta ki aiwatar da Naira 35,000 ba ta da sauran samun zaman lafiya. Wannan shine ra’ayina.”
Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye
https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx
Torawa Yan'uwa Da Abokai