Gari ya waye ta rawaito cewa Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC) ta ce ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) ga dalibai masu zaman kansu.
An gudanar da jarrabawar tsakanin 27 ga Oktoba zuwa 20 ga Disamba 2023.
WAEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar, Moyosore Adesina, a ranar Talata, 13 ga watan Fabrairu.
Sanarwar ta ce, jimillar dalibai 85,600 ne suka yi rajistar jarrabawar amma 80,904 ne suka zana jarrabawar a cibiyoyi 568 a fadin kasar nan.
WAEC ta ce jimillar dalibai 39,790, wanda ya kai kashi 49.18 cikin dari maza ne, yayin da 41,114, wanda ke wakiltar kashi 50.82 cikin 100 mata ne.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, masu rubuta Jarrabawa duba saba’in da takwas da dari hudu da shatara 78,419, wadanda ke wakiltar kashi 96.93 cikin 100 ne aka kammala tantance sakamakonsu kuma aka fitar da su, yayin da mutum 2,485, wadanda ke wakiltar kashi 3.07 cikin 100, har yanzu ake ci gaba da tantance wasu daga cikin batutuwan da suka shafi sakamakon akan wasu kura-kurai da aka samu.
Hukumar WAEC, ta ce an rike sakamakon dalibai 7,192 da ke wakiltar kashi 8.89 bisa 100 da ake zargi da aikata wasu laifuka.
Domin samun labarai da dumi-dumin su. Latsa wannan link.👇🏻👇🏻👇🏻
https://t.me/labarangariyawaye
Torawa Yan'uwa Da Abokai