KanunLabarai

Hukumar Hisbah Ta Kama Shahararriyar Yar’ TikTok A Kano Bisa Zargin Badala

Gari Ya Waye ta rawaito cewa Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama fitacciyar Yar’ TikTok Murja Ibrahim Kunya, bisa zargin aikata badala.

Aliyu Usman, shugaban rundunar ‘Operation ‘Kau da badala’ wanda ke rike da mukamin jami’in sa ido, ya tabbatar wa Aminiya kamun.

Ya ce, “An kama ta ne shekaran jiya (Litinin) da yamma a gidanta da ke unguwar Tinshama. Kusan awa uku muka yi muna jiran ta kafin daga bisani ta fito muka dauke ta.

“An tuhume ta da wasu ayyukan lalata da suka saɓa da dokokin jahar Kano. Akwai wanda kullum yakan zo ya dauke ta da misalin karfe 10 na dare kuma zai dawo da ita da karfe 12 na dare ko 1 na safe.”

Ya kara da cewa za a gurfanar da Kunya a gaban kotun shari’ah da ke zama a PRP ranar Talata.

Aminiya ta rawaito cewa Hukumar Hisbah ta kaddamar da farautar akalla mashahuran ’yan Tiktok su shida da ake zargi da yada bidiyoyi na batanci a shafukan sada zumunta.

Wannan na zuwa ne ‘yan watanni bayan da babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya gayyaci daukacin mata ‘yan Tiktok da ke Kano zuwa wani zama inda hukumar ta yi tayin gyarawa da karfafa musu sana’o’i da tallafin karatu.

A wajen taron, Sheikh Daurawa ya hori daukacin ‘yan Tiktok da sauran masu sha’awar shafukan sada zumunta da su daina yada abubuwan da za su iya karfafa lalata a cikin al’umma.

Domin samun labarai da dumi-dumin su. Latsa wannan link Na Telegram channel.👇🏻👇🏻👇🏻

https://t.me/labarangariyawaye

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *