Photo credits: Daily post
Kocin Super Eagles Jose Peseiro ya magantu kan damuwar da wasu masoya kollon kafa ‘yan Najeriya ke nunawa ta rashin buga wasa da kyaftin ɗin Super Eagles Ahmed Musa. Wasu na ganin yana da kyau ko a karshen wasa a dan bashi dama a matsayin sa na jagoran tawagar yan’wasan.
Ahmed bai buga ko wasa guda ba cikin wasanni huɗu da suka buga a gasar Afcon ta 2023 da ke gudana a Côte d’Ivoire.
Amma kocin ya ce duk da rashin buga wasan da Ahmed ke yi yana da amfani a cikin tawagar.
“Zai iya buga wasa, amma abin da mutane ya kamata su sani shi shugaba ne,” kamar yadda Peseiro ya bayyana a taron manema labarai da ake yi idan an kammala wasa.
Ya jadda cewa zaman Musa a benci shi kan shi wata dama ce musamman ga matasan ‘yan wasan tawagar, tun da suna yi masa kallon abin koyi.
“Gudunmuwarsa ta kasu kashi biyu, ta cikin fili da kuma ta waje. Idan ba shi da amfani da ba mu kira shi ba tun da fari,” in ji kocin.
Source Idongari
Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye
https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx
Torawa Yan'uwa Da Abokai