KanunLabarai

Matsala Ga Ma’aikatan Tarayya Yayin Da Gwamnati Ta Kasa Biyan Albashi.

Ana samun karuwar tashe-tashen hankula a tsakanin ma’aikatan gwamnatin tarayya, ma’aikatu, da hukumomi, da MDA, kan rashin biyan albashin watan Janairu.

Al’amarin ma’aikatan ya kara dagulewa da yadda suma suna bin bashin kudin tallefi na dubu talatin da biyar N35,000.

An tattaro cewa rashin biyan albashin watan Janairu ga manyan ma’aikatan gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba ya biyo bayan gazawar ofishin Akanta Janar na kasa, OAGF, wajen kammala kasafin kudin shekarar 2024 kan hada-hadar kudi na gwamnati. Tsarin, GIFMIS.

Rashin nasarar ya hana fitar da sammacin ma’aikata na Janairu 2024 don biyan albashi.

Babban sakataren kungiyar ma’aikatan Najeriya, NCSU, Bomoi Muhammed Ibraheem, ya tabbatarwa da jaridar Vanguard cewa ba’a biya ‘ya’yan kungiyar albashi ba.

Wata sakatariyar ma’aikata a Abuja, wacce ta koka da lamarin, ta shaida wa Vanguard cewa: “Ma’aikatan gwamnatin tarayya sun ji takaicin jinkirin biyan albashin watan Janairu. Kowa ya san abin da ke faruwa a Najeriya a yau.

“Halin da ake ciki na tattalin arziki ba zai iya jurewa ba, duk saboda manufofin gwamnati. N35,000 da aka yi alkawari bayan cire tallafin man fetur sai a watan Satumba. Yanzu, gwamnati ta ki biyan mu albashin watan Janairu, wanda hakan ya kara tsananta mana.

“Ta yaya suke tsammanin mu cika nauyin da ke kanmu ga iyalanmu da suka hada da kudin makaranta da sauran abubuwan bukatu? Ba za mu iya ci gaba a haka ba.”

Don kawar da tsaikon da ma’aikatan ta ke yi, hukumar gudanarwar cibiyar ilmin lissafi ta kasa, Abuja, a cikin wata sanarwa ta cikin gida mai dauke da kwanan watan 31 ga watan Janairu, 2024, mai taken “ Jinkiri wajen biyan albashin Janairun 2024”, da sauran su sun ce “Muna so mu sanar da ku cewa. Janairu 2024 albashi za a jinkirta fiye da yadda aka saba.”

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *