KanunLabarai

Gwamnatin Kano ta ƙayyade wa makarantu masu zaman kansu kudaden Jarabawar WAEC da NECO.

Gari ya waye ta rawaito mashawarcin gwamnan kano, akan makarantun masu zaman kansu dana sa-kai, Honourable Baba Abubakar Umar Tarauni, cikin wata takarda da aka raba wa manema labarai, me ɗauke da sa hannun Daraktan tsare-tsare da ƙididdiga na Hukumar Malam Hamisu Muhammad.

Takardar ta bayyana cewa Gwamnatin kano ta ƙayyade naira dubu Arba’in da biyar ₦45,000 a matsayin kuɗi mafi yawa da makarantu masu zaman kansu dana sa-kai zasu karɓa daga wajen iyayen yara a fadin jihar kano, a matsayin kuɗin jarabawar WAEC ko NECO.

Takardar ta ƙara da cewa, gwamnatin Kano karkashin Mai girman Gwamna Abba Kabir Yusuf ta dauki wannan mataki ne, biyo bayan rahotan da ta samu na wata makaranta ta ƙayyade naira dubu ɗari biyu da Hamsin ₦250,000 a matsayin kuɗin da zata karɓa daga Wajen iyayen yara domin yin jarrabawar WAEC da NECO.

Saboda haka ne gwamnatin kano tace, kada makarantar da ta karɓi abin da ya haura Naira dubu arba’in da biyar ₦45,000 na kowacce jarrabawar, wanda ya kunshi kudin rijista da sauran shirye-shirye.

Daga karshe Gwamnatin kano, tayi fatan dukkan makarantu masu zaman kansu dana sa-kai dake fadin jihar zasu yi biyayya ga wannan doka.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *