KanunLabarai

Jami’an Tsaro Sun kama Matar da ta Jagoranci Zanga-zangar Lumana Akan Tsadar Fulawa a Kano.

Jami’an Tsaron Yan Sanda sun kama matar nan Fatima Auwal wadda ke unguwar Ceɗiyar ‘yan gursa, bayan da ta jagoranci Zanga-zanga akan tsadar Fulawa a Kano.

Jaridar SOLACEBASE ta Rawaito cewar, ‘Yan Sandan sun kamata a sakamakon ƙarar ta da wasu mata biyu da namiji daya suka yi a caji-ofis din Jakara, bisa zargin Fatima ba ‘yar Ƙungiyar su bace, saboda haka ne masu ƙorafin suka ce ba tada hurumin jagorantar Zanga-zangar da sunan ƙungiyar su.

Sai da kuma tuni ita Fatima Auwal ta musanta zargin, inda tace waɗanda suka yi ƙorafin ‘yan tallan Gurasa ne ba masu sarrafa ta ba.

A Martanin da Shugaban ƙungiyar masu sana’ar Gurasa Na Sha tale-talen Jakara (Jakara Junction Gurasa Bakers, Multi-Purpose Cooperative Society), ya mayar, Hadiyyatulahi Hamisu yace babu shakka sune suka yi ƙararta saboda tayi amfani da sunan ƙungiyar su.

Malam Hamisu ya ƙara da cewa ita Fatima me yin Gurasa ce kuma Shugabar wani rukuni ce ta masu sana’ar Gurasa, bawai ita ce Shugabar masu yin Gurasar gaba-ɗaya ba, saboda haka suka yi ƙarar ta domin ta shiga kafafen yaɗa labarai ta janye kalamanta.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

FACEBOOK PAGE:

https://www.facebook.com/profile.php?id=61555682938654&mibextid=9R9pXO

X PAGE (TWITTER)

https://x.com/gariyawaye01?t=iPkME2Ddq50H0i5Qf20phw&s=09

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *