KanunLabarai

Sake Zabe: Jam’iyyar NNPP ta lashe kujeru biyu na ‘yan majalisar jiha a Kano

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Dr Alhassan Zakariya Ishaq na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Kura/Garun Mallam da ke Kano.

Gari ya waye ta ruwaito cewa jami’in zabe na jihar Farfesa Shehu Musa Galadanchi ya bayyana cewa Ishaq na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 37,262 inda ya doke Musa Hayatu Daurawar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wanda ya samu kuri’u 30,803.

Idan ba a manta ba kotun daukaka kara ta umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 20 da ke mazabar Kura/Garun Malam a jihar Kano.

Hakazalika, INEC, ta ayyana Bello Muhammad Butu-Butu na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi ranar Asabar a mazabar Rimin Gado/Tofa.

Jami’in da ya lashe zaben Farfesa Ibrahim Tajo Suraj ya kuma bayyana cewa Bello Muhammad Butu-Butu na jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 31,135 inda ya doke abokin takararsa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, wanda ya samu kuri’u 25,577.

Kotun daukaka kara ta kuma umurci INEC da ta sake gudanar da zabe a rumfuna 33 da ke mazabar jihar Rimin Gado/Tofa.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

FACEBOOK PAGE:

https://www.facebook.com/profile.php?id=61555682938654&mibextid=9R9pXO

X PAGE:

https://x.com/gariyawaye01?t=iPkME2Ddq50H0i5Qf20phw&s=09

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *