KanunLabarai

LABARAI: NLC, TUC sun fitar da sanarwar yajin aiki da zai shafi fadin kasa.

Kungiyoyin kwadagon Najeriya (TUC) da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC sun aike da sanarwar gargadi na kwanaki 14 ga gwamnatin tarayya.

Kungiyoyin sun ce yarjejeniyar mai dauke da abubuwa 16 da aka cimma a ranar 2 ga watan Oktoban 2023 tsakaninsu da gwamnatin tarayya ba a aiwatar da su ba.

Shugabannin kungiyoyin TUC da NLC na kasa sun bayyana bakin cikin su kan yadda gwamnati ke nuna halin ko-in-kula da wahalhalun da al’umma ke ciki, duk da kokarin da suke yi na wanzar da zaman lafiya a masana’antu.

Kungiyoyin kwadagon a cikin wata sanarwa sun ce: “Yarjejeniyar ta ranar 2 ga Oktoba ta mayar da hankali ne kan tinkarar bala’in wahala da kuma mummunan sakamako na zamantakewar al’umma na rashin tunani da rashin aiwatar da IMF/Bankin Duniya da ya jawo tashin farashin PMS da kuma faduwar darajar farashin naira. Wadannan tsare-tsare guda biyu, kamar yadda muka yi hasashe, sun yi mummunar illa ga tattalin arzikin talakawa da ma’aikatan Najeriya.”

Sun kuma koka da cewa: “Abin takaici ne yadda aka tilasta mana daukar irin wadannan matakan, amma rashin kula da jin dadin ‘yan kasa da ma’aikatan Najeriya da kuma tsananin wahala ya sa ba mu da wani zabi.

“Sakamakon wannan ci gaba tare da sanin muhimmancin tabbatar da tsaro da kare hakki da mutuncin ma’aikatan Najeriya da ‘yan kasa, kungiyar NLC da TUC sun ba da wani babban wa’adi ga gwamnatin tarayya da ta karrama bangaren su. Domin samun fahimta a cikin kwanaki 14 daga gobe, ranar 9 ga Fabrairu 2024.”

 

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *