KanunLabarai

Kisan Kai: Shari’ar Hafsat Chuchu Ta Ɗauki Wani Sabon Salo A Yau Alhamis

Shari’ar da ake zargin Hafsat Surajo Chuchu da zargin kashe abokin kasuwancin ta Nafi’u Hafiz, a gaban babbar kotun jahar Kano mai namba 13 karkashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf, ta dauki wani sabon salo, bayan an karanto mata kunshin tuhumar har sau bakwai amma ta yi gum da bakin ta taki cewa komai.

Alfijir labarai ta rawaito an gurfanar da mijin Hafsat Surajo Dayyabu Abdullahi da Mal Adamu Mohd da kuma Nasidi Muhammed, wadanda ake tuhuma da laifin boye gaskiyar abunda ya faru game da mutuwar Nafi’u, da kuma bayar da bayanan karya wanda yin hakan ya saba da sashi na 167 na kundin Penal Code.

Yayin da jami’in kotun Bashir Bello Fagge ya karanto wa Hafsat Surajo kunshin tuhumar aikata laifin kisan kai ta hanyar caccaka wa Nafi’u wuka a sassan jikinsa, karkashin sashi na 221 na dokar kasa, har sau bakwai ana karanta mata inda ki yin Magana.

Da farko mai shari’a Zuwaira Yusuf ta ce a bata Dama sakamakon ta yi gum da bakin ta ko wani abune ya hanata yin Magana, bayan an dawo an sake karanta mata tuhumar nan ma taki cewa komai.

Lauyar gwamnatin jahar Kano A’isha Mahmud ta roki kotun akai wadda ake tuhumar ta farko asibiti domin a duba kwakwalwarta sakomakon kin cewa komai da ta yi.

‘’Idan an samu irin hakan, wanda ake tuhuma ya yi shiru a shari’a ana bayar da dama a duba kwakwalwarsa , zai iya yiwuwa ne, ya yi hakan saboda keta ko kuma rashin lafiya’’

Sai dai koda aka karanto wa Dayyabu Abdullahi, Adamu Mohd da kuma Nasidi Muhammed, kunshin zargin boye gaskiyar mutuwar Nafi’u da kuma bayar da bayan karya sun amsa da cewar sun fahimci abunda ake tuhumarsu.

Lauyan dake kare wadanda ake tuhuma na 1,2 da na 3 barista Haruna Magashi ya bayyana cewa, wadda ake zargi ta farko taki yin magana domin ba ta ce Eh ko a a ba.

Barista Magashi ya kara da cewa bisa zargin ake yi ko suna da hannu wajen hana ta yin magana ya ce basu da hannu.

Lauyoyin wadanda ake tuhuma 2,3 da na 4, sun nemi a bayar da belinsu, sai dai kotun ta jinkirta yin hukunci kan rokon beli ko akasin haka zuwa nan gaba.

Mai shari’a Zuwaira Yusuf ta bayar da umarni ga likitan dake gidan gyaran hali da tarbiya na Goron Dutse ya binciki lafiyar kwakwalwar Hafsat Surajo, sakamakon kin yin Magana bayan karanto mata kunshin tuhumar har sau bakwai.

Credits to: alfijirlabarai.com

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *