KanunLabarai

Shari’ar Kisan Nafi’u da ake zargin  Hafsat Chuchu Ta Samu Tsaiko.

Photo credits: HausaLoaded.com

Shari’ar zargin Hafsat Suraj wadda ake kira da (Chuchu) da wasu maza mutum uku kan zargin kashe wani mai suna Nafiu Hafiz da ke gaban Babbar Kotun Jihar Kano ta samu cikas.

Shari’ar da a ke gabatarwa a babbar kotun jahar Kano, da ke zamanta a titin Miller karkashin jagorancin Mai sharia Zuwaira Yusuf ta samu tsaiko ne sakamakon rokon da bangaren wadanda ake zargi ga kotun ta dege shari’ar sannan ta sanya musu wata rana da za a dawo domin karanta wa wadanda ake kara takardar tuhumarsu.

Sudai Wanda ake tuhumar sun hada da Hafsat Chuchu da mijinta da mai gadinsu da kuma malamin da ake zargi da yi wa gawar Nafiu wanka.

Tun da farko an taba gurfanar da su gaban kotun Majistare da ke zamanta a ’Yankaba karkashin jagorancin Mai Shari’a Hadiza Abdurrahman inda ake tuhumar Hafsat Chuchu da kisan Nafiu Hafiz, sukuma sauran wato mijinta  da marigayi da kuma Malam ake tuhumar su da laifin boye gaskiyar dalilin rasuwar Nafiu.

Tunda farko bangaren masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Aisha Mahmud sun nemi kotun ta yarje mu su, don musanya takardar karar da wata sabuwa, kasancewar sunan wanda ake zargi na hudu, ba ya cikin tsohuwar takardar rokon da kotun ta amince da shi.

Amma bangaren masu kariya karkashin jagorancin Barista Huwaila Ibrahim Muhammad sun nemi kotun ta sanya wata rana don sake gurfanar da wadanda ake zargin a gabanta domin su da wanda suke karewa na hudu su samu damar yin nazarin takardar karar.

Kotun ta sanya ranar Alhamis 8 ga watan Fabarairun 2024 don gabatar da wadanda ake tuhumar.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *