KanunLabarai

Wata kungiya a Jahar Kano ta bukaci majalisar dokokin Jahar ta rusa masarautu, a mayar da Khalifa Sanusi

Wata kungiya a jihar Kano ta bukaci da a rusa masarautun jihar Kano guda hudu, wanda suka hada da masaurautar Bichi, Rano, Gaya da Karaye sannan a mayar da tsohon sarki Muhammadu Sanusi na II a matsayin sabon sarkin Kano.

GARI YA WAYE, ta rawaito cewa kungiyar mai suna ‘Yan Dangwalen Kano ta bukaci gwamnan Kano da majalisar dokokin jihar su duba sashen dokar da ya rarraba masarautar Kano zuwa masarutu guda biyar.

Wannan Kungiya mai sauna kungiyar ‘yan dangwale ta ce masarauta guda daya kamar yadda take a baya zai taimaka wajen tafiyar da harkar sarauta ba tare da rarrabuwar kai ba. Sannan hakan zai karawa sarautar kima da samar da zaman lafiya mai dorewa.

Maganar tsohon sarki, Muhamamdu Sanusi II, kuma sanarwar ta ce “Bisa girmamawa muna kira ga majalisar dokoki ta jihar Kano da ta yi waiwaye dangane da sashen dokar da ya kwabe Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki. Mun yi amannar cewar tunbuke Sanusi Lamido Sanusi ya haifar da rashin zaman lafiya a jihar”.

A karshe kungiyar ta bukaci majalisar dokokin jahar Kano da ta yi nazari kan bukatunta domin ci gaba da zaman lafiya da karuwar arzikin jama’ar jahar Kano.

Domin samun sahihan labarai shiga WhatsApp group na labarangariyawaye

https://chat.whatsapp.com/DJEjSDGhJeX3PHx7XzXeHx

Torawa Yan'uwa Da Abokai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *