Gwamnatin Najeriya Ta Gayyaci Kamfanonin Dangote, BUA, Lafarge Kan Karin Farashin Siminti
Gwamnatin Najeriya ta gayyaci daukacin kamfanonin da ke samar da siminti a kasar zuwa wata…
Gwamnatin Najeriya ta gayyaci daukacin kamfanonin da ke samar da siminti a kasar zuwa wata ganawa da ministan ayyuka David Umahi, kan tashin farashin kayayyakin masarufi a kasuwa. An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai ba wa Ministan shawara na musamman Edward Uchenna Orji ya fitar a ranar Asabar. Gari Ya Waye ta…
Joe Ajaero, shugaban kungiyar NLC ne ya bayyana haka a gidan ma’aikata dake Abuja, yayin wani taron gaggawa, wanda aka gudanar a ranar Juma’a. Ajaero ya ce an dauki matakin gudanar da zanga-zangar ne bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da aka baiwa gwamnatin tarayya kan wahalhalun da kasar ke fuskanta. Gari ya waye ta ruwaito…
Gari ya waye ta ruwaito cewa, a ranar Juma’ar da ta gabata ne Hukumar Kare hakkin masu sayen kaya ta Tarayya, ta rufe Sahad Store, wani shahararren kantin sayar da kayayyaki da ke unguwar Garki a Abuja. Hukumar ta FCCPC ta ce an rufe shagon ne saboda rashin nuna gaskiya kan yadda yake kayyade farashin…
A daren Laraba da safiyar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kaddamar da ta’addanci a fadin jihar Katsina, inda suka kai hari a wani masallaci, da gidaje, tare da yin asarar rayuka da kuma yin garkuwa da su. Lamarin da ya fi kamari ya faru ne a lokacin Sallar Isha’i a kauyen…
‘Yan majalisar dokokin Najeriya sun yi watsi da kudirin dokar da ke neman a daukaka darajar ilimi a manyan mukaman siyasa a kasar. A yayin muhawarar da aka yi a zaman majalisar wakilai a ranar Talata, Onanuga ya bayyana cewa ilimi mai zurfi na da matukar muhimmanci ga ingantaccen jagoranci. A tsaye da sunan Adewunmi…
Gari Ya Waye ta rawaito cewa Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama fitacciyar Yar’ TikTok Murja Ibrahim Kunya, bisa zargin aikata badala. Aliyu Usman, shugaban rundunar ‘Operation ‘Kau da badala’ wanda ke rike da mukamin jami’in sa ido, ya tabbatar wa Aminiya kamun. Ya ce, “An kama ta ne shekaran jiya (Litinin) da yamma…
Gari ya waye ta rawaito cewa Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC) ta ce ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) ga dalibai masu zaman kansu. An gudanar da jarrabawar tsakanin 27 ga Oktoba zuwa 20 ga Disamba 2023. WAEC ta bayyana hakan ne a cikin wata…
Gari ya waye ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan Sanata mai wakiltar Imo-North Senatorial District (Okigwe zone), Sanata Patrick Ndubueze, wanda ya yi sanadin mutuwar daya daga cikin mai tsaronsa sa. Wata majiya da ke kusa da Sanatan ta shaida wa majiyarmu ta kasa cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan…
Mai shari’a Umaru Fadawu na babbar kotun jihar Borno da ke zamanta a Maiduguri a ranar Litinin 12 ga Fabrairu, 2024, ya yanke wa Aisha Wakil (wacce aka fi sani da Mama Boko Haram), Tahiru Daura da Lawal Soyade daurin shekaru 10 a gidan yari. An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugaban…
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bukaci uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, da ta shaida wa shugaban kasa Bola Tinubu halin da ake ciki na yunwa da fatara a kasar nan. “Duk da cewa muna da hanyoyi da dama na isar da sako ga gwamnati kan bukatunmu da bukatun al’umma, amma hanyarku da hanyoyinku…