Shugaba Tinubu ya ba da umarnin a gaggauta sakin Tan 102,000 na shinkafa da masara ga ‘yan Najeriya don rage wahalhalu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a gaggauta sakin sama da tan dubu 102 na nau’in hatsi iri-iri daga asusun ajiyar abinci na kasa da kuma kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya. An ce umarnin wani martani ne na wucin gadi da gwamnatin ta yi kan matsalar karancin abinci da ake fama da shi…